Manhaja mai illa ga na'ura mai kwakwalwa a tashar nukiliyar Iran

Tashar nukiliyar Bushehr
Image caption Tashar nukiliyar Bushehr

Wani babban jami'in kasar Iran yace, manhaja mai yin lahani ga na'ura mai kwakwalwa ta harbi wasu daga cikin na'urori masu kwakwalwa na kasar, a cibiyar sarrafa makamashin nukiliya dake Bushehr, amma ya kara da cewa na'urorin suna nan daram babu matsala.

Wannan manhaja wadda ake kira da sunan Stuxnet, ta harbi na'urori masu kwakwalwa a Indonesia, India da Pakistan, amma Iran ce ta fi gamuwa da wannan matsala.

Wani wakilin BBC ya ce, masana kan na'ura mai kwakwalwa na ganin cewa, irin basirar da aka yi amfani da ita wajen tsara wannan manhaja mai lahani, zai iya zama wani bangare na tuggun kasashen yamma, domin yin makarkashiya ga shirin nukiliya na Iran.