Tattaunawar zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

Shugabannin Isra'ila da Falasdinawa tare da Hillary Clinton
Image caption Shugabannin Isra'ila da Falasdinawa tare da Hillary Clinton

Gwamnatin Isra'ila ta bayyana cewa tana yunkurin cimma maslaha da shugabannin Falasdinawa a daidai lokacin da batun ci gaba da gina matsugunan Yahudawa ke barazana ga tattaunawar kawo zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ministan tsaron Isra'ila, Ehud Barak, wanda shi ne jami'in da ke jagorantar tawagar Isra'ila a tattaunawar, ya shaidawa BBC cewa zai yi kokarin shawo kan abokan aikinsa a gwamnati, da fatan za su sulhunta da Falasdinawa a kan batun gina matsugunan Yahudawan, ko da ya ke babu tabbas zai yi nasara.

Sai dai ya ce yana fatan ko ma menene ya faru tattaunawar da ake yi don kawo zaman lafiya za ta ci gaba.

Bangarorin biyu dai sun dage a kan matsayin da suka dauka a kan batun.

Yayin da hukumomin Isra'ila ke cewa nan gaba a yau wa'adin dakatar da gina matsugunan zai kare, Falasdinawa kuwa cewa su ke yi muddin aka ci gaba da gine-ginen za su kauracewa tattaunawar.

Yahudawa 'yan share-wuri-zauna, wadanda ke samun goyon bayan gwamnatin hadin gwiwa ta Isra'ila, sun sha alwashin ci gaba da gine-ginen a yau.

Shi kuwa Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya tsinci kansa ne a halin gaba kura baya siyaki: idan ya sassauta matsayinsa a kan batun, kallon da Falsadinawa ke yi masa na shugaba mai rauni zai tabbata; idan kuma ya kauracewa tattaunawar za a zarge shi da yiwa shirin zaman lafiyar kafar ungulu.

Karin bayani