Gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya na bayan Goodluck Jonathan

Goodluck Jonathan, Shugaban Najeriya
Image caption Goodluck Jonathan, Shugaban Najeriya

A Najeriya gwamnonin jihohi biyar na shiyyar kudu maso gabashin kasar - watau Abia da Anambra da Ebonyi da Enugu da kuma Imo - sun bayyana goyon bayansu ga takarar shugaba Goodluck Jonathan a zabe mai zuwa.

Gwamnonin sun kuma bukaci sauran jama'ar shiyyar da su mara masa baya a zaben shugaban kasar da za a yi a shekara mai zuwa.

Sun yanke shawarar ce a karshen wani taro da suka kammala yau a birnin Enugu.

Yayin da a makon gobe ake sa ran kwamitin da dattawan arewacin Najeriyar su ka kafa zai yi zama, don fitar da wanda zai yiwa yankin takara a zaben na badi, wata kungiya mai ikirarin kishin Arewan, Northern Patriots, ta yi kira ga mambobin kwamitin da kada su yi zaben tumun dare.