Kasashen Duniya na kara hurawa Israila wuta

Gine Ginen matsugunnan Yahudawa
Image caption Gine Ginen matsugunnan Yahudawa

Ma'aikatar kula da harkokin wajen Amurka, ta bayyana rashin jin dadinta game da shawarar da Isra'ila ta yanke ta kin kara wa'adin dakatar da gina matsugunnan yahudawa a yankunan da ta mamaye.

Shugabannin Palasdinawa sun ce ba zasu mayar da martani ba, har nan da tsawon mako guda, game da yadda Isra'ila ta kawo karshen dakatar da gina matsuguna Yahudawa a gabar yammacin Kogin Jordan.

Jiya da karfe sha biyun dare ne, wa'adin da Isra'ilar ta shata wa kanta, na dakatar da gine ginen ya cika.

Jagoran Palasdinawa Mahmud Abbas ya ce ba ya tsammanin shawarwarin sulhun da aka farfado da su, zasu dore, matukar ba Isra'ila ce ta dakatar da ci gaba da gine ginen ba.

Tuni dai wasu Yahudawa 'yan kama-wuri zauna suka fara kafa harsashin gine ginen.

Wakilin Amurka na musamman a gabas ta tsakiya, George Mitchell na kan hanyarsa ta zuwa yankin domin ganawa da Shugabannin Isra'ila da yankunan Palasdinawa.