Rashin tabbas a gabas ta tsakiya

tattaunawar sulhu a gabas ta tsakiya
Image caption rashin tabbas a tattanawar sulhu na gabas ta tsakiya

Wani babban jami'in Palasdinawa ya shaidawa BBC cewa nan zuwa da jibi Laraba, zasu tsayar da magana kan ko zasu janye daga tattaunawar sulhu a yankin gabas ta tsakiya.

Nabil Shaath wani babban mamban Palasdinu dake cikin tawagar dake tattaunawar ya ce za su dauki mataki akan ko shin zasu cigaba da tattaunawar, amma sai bayan shugabannin Palasdinu sun gana a birnin Ramallah a ranar Laraba mai zuwa.

Shugaba Mahmoud Abbas dai na kan wani mawuyacin mataki, kuma za'a iya tilasta masa ya bayar da kai domin bori ya hau.

Tun makwanni da dama da suka shude ne dai yake ta nanata cewa ya zama lallai a dakatar da gina matsugunnan yahudawa a yankunan Palasdinu.

Shugaba Abbas, dai ya yi kira ga Israela da su zabi a zauna lafiya:

Yace zabi guda ne kadai ya yi saura, ko dai gine-gine ko kuma zaman lafiya. Ya kamata Israela ta zabi zaman lafiya, idan kuma har Israelar ta zabi zaman lafiya, to zamu cigaba da tattaunawa, amma idan kuwa ba ta zabi haka ba, to wannan zai kasance bata lokaci, ko kuma wata dama da ta kubce.

Sai dai Israela ta ki amincewa da haka. A wani sako da Prime Ministan Israela Benjamin Netanyahu wanda ya biyo ta hannun mai magana da yawunsa wato Mark Regev, ya bayyana cewa bai kamata Palasdinawa su yi fatali da tattaunawar zaman lafiya ba, duk kuwa da cikar wa'adin.