Ba za mu yi gaggawa ba: Shugaban Falasdinawa

Aiki a daya daga cikin matsugunan Yahudawa a birnin Kudus
Image caption Aiki a daya daga cikin matsugunan Yahudawa a birnin Kudus

Shugaban Falatsdniwa Mahmoud Abbas, ya ce ba zai yi gaggawar yanke shawara kan ko za su janye daga tattaunawa da Isra'ila ba, sai bayan ya gana da shugabannin kasashen Larabawa a mako mai zuwa.

Mista Abbas na magana ne bayanda wa'adin wucin gadin da Isra'ila ta sanya na dakatar da sabbin gine-gine a yankin Yahudawa 'yan kama wuri zauna na gabar Yammacin kogin Jordan ya kare.

Shi dai Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ki amincewa da bukatun kasashen duniya na kara wa'adin dakatar da gine-gine a matsugunan Yahudawa da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan, inda Isra'ilar ta mamaye.

Da ma dai Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya ce dakatar da gina matsugunan Yahudawan ne kawai zai sa ya ci gaba da tattaunawar kawo zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Amma duk da matsin lambar kasashen duniya, musamman Amurka, Isra'ilar ba ta kara wa'adin dakatar da gine-ginen ba.

Abin da Firayim Minista Netanyahu ya yi kawai shi ne kira ga Yahudawa 'yan kama wuri zauna su yi taka-tsantsan.

To amma duk da wannan kira—tun ma kafin wa'adin ya ida cika—Yahudawan da ke daya daga cikin yankunan suka fara aza harsashin gina wata makarantar nursery.

Firayim Minista Netanyahu ya kuma bukaci Shugaba Mahmoud Abbas ya daure ya ci gaba da tattaunawar.

To amma Mista Abbas ya ce sai ya yi shawara da shugabannin kasashen Larabawa, wadanda ake sa ran zai gana da su nan da kawanaki goma masu zuwa, kafin ya yanke hukunci a kan matakin da zai dauka.

Har yanzu dai masu shiga-tsakani a karkashin jagorancin Amurka suna ta hankoron ganin tattaunawar ba ta durkushe ba.

A halin da ake ciki dai makomar tattaunawar, wadda aka fara wata guda da ya gabata, ta dogara ne a kan sakamakon ganawar ta Shugaba Mahmoud Abbas zai yi da shugabannin kasashen Larabawa.

Karin bayani