Majalisar dokoki ta bukaci karin bayani daga hukumar zabe

Prof Attahiru Jega
Image caption Prof Attahiru Jega

Kwamitin kula da yiwa tsarin mulkin Nigeria garanbawul, ya baiwa hukumar zaben Nigeria mai zaman kanta zuwa ranar laraba da ta gabatar da hujjojinta dalla dalla akan dalilan da suka sa ta ke neman karin lokaci na gudanar da zabe.

Kwamitin ya baiwa hukumar wannan wa'adi ne bayan wata ganawa tare da shugaban hukumar zaban mai zaman kanta, Farfesa Attahiru Jega.

Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewar, hukumar na neman wannan kari ne, domin samu ta gudanar da sabuwar rajista da zata baiwa hukumar damar yin sahihin zabe.

Tun farko dai jam'iyyun siyasa a Nigeriar, sun yi na'am da bukatar karin lokacin, suna cewar yin hakan zai basu damar kammala shirye shiryensu a tsanake.

A karkashin dokar zabe ta 2009, za'a gudanar da zaben ne a cikin watan Jainaru. na shekara mai zuwa