Majalisun Nigeria na taro da INEC

INEC na neman a daga lokacin zabe
Image caption Hukumar zaben Nigeria na neman a matsar da lokacin zabe

Kwamitin gyaran-fuska ga Kundin tsarin mulkin Nigeria na wani zaman gaggawa da shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Attahiru Jega domin sauraron bukatar da hukumar ta gabatar ta neman a matsar da babban zaben kasar daga watan Janairu zuwa Afrilun badi.

Wani taro da aka gudanar tsakanin hukumar zaben ta kasa INEC da jam'iyyun siyasar Nijeriyar cikin makon jiya ya amince da a sauya lokacin zaben.

A tattaunawarsu da Ibrahim Isa, shugaban hukumar zaben ya jaddada cewa sai an tura zaben gaba ne za su samu damar yin rajistar masu kada kuri`a cikin natsuwa, wadda kuma za ta taimaka wajen gudanar da zabe mai inganci.

Dangane da batun rajistar masu zabe kuwa, shugaban hukumar zaben Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa, suna bukatar lokaci domin yin odar naurorin tare da gudanar da aikin rajistar.

Wannan ne a cewarsa, daya daga cikin dalilanda suka sanya hukumar ke bukatar karin lokacin gudanar da zaben.