Kungiyar NATO ta kai hare-hare a Pakistan

Dakarun NATO suna sintiri a Afghanistan
Image caption Dakarun NATO suna sintiri a Afghanistan

Wasu dakarun kungiyar kawance ta NATO sun kai hare hare akalla biyu ta tsallaken kan iyaka kan wadanda ake kyautata zaton masu tayar da kayar baya ne a cikin Pakistan.

Wani mai magana da yawun rundunar dakarun ISAF da ke karkashin kungiyar ta NATO a Afghanistan ya tabbatar da cewa wasu jirage masu saukar angulu na kungiyar sun shiga cikin hare haren da aka kai a karshen mako, inda kuma aka kashe sama da mutane hamsin.

Duk da cewar akan tura jiragen saman yaki da babu matuka a cikinsu, domin kai hare hare a kan mayakan sa kai, ba kasafai NATO ke fitowa ta amsa cewar dakarunta sun shiga sararin samaniyar Pakistan ba.