Gabashin Najeriya na goyon bayan Jonathan

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

A Najeriya, gwamnonin jihohi biyar na shiyyar kudu masu gabashin kasar, sun bayyana goyon bayansu ga takarar Shugaba Goodluck Jonathan a zabe mai zuwa.

Wannan shawara da gwamnonin suka yanke a karshen wani taro da suka gudanar a daren jiya a birnin Enugu, ta biyo bayan gamsuwar da suka ce sun yi ne, cewa shugaban kasar ya dace da irin dan takarar da suke neman mara wa baya.

Shugaban taron, kuma gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya bayyana cewa:

“Kamar yadda muka yanke shawara tun da farko, cewa za mu mara baya ne ga dan takarar da ke da kyakkyawan shiri na warware matsalar mayar da shiyyar kudu maso gabas saniyar ware, mun yanke shawarar mara baya ga neman shugabancin kasar nan da Shugaba Goodluck Jonathan ke yi a zabe na gaba”.

Ana dai ganin cewa matakin da Shugaba Jonathan ya dauka na mayar da filin saukar jiragen sama na Enugu na kasa-da-kasa da kuma yunkurin magance matsalar zaizayar kasar da ta addabi yankin ne suka jawo hankalin gwamnonin wajen ba shi goyon baya.

Sai dai wadansu masu lura da al’amura na ganin shawarar gwamnonin na da illa a siyasance.

A ganin masu irin wannan ra’ayi dai, marawa Shugaba Jonathan baya ka iya yin kafar ungulu ga yunkurin da al’ummar yankin ke yi na ganin dan kabilar Ibo ya dare kujerar shugabancin kasar a shekarar 2015.