An gargadi gwamnatin Burtaniya

Firayim Minista David Cameron na Burtaniya
Image caption Firayim Minista David Cameron na Burtaniya

An gargadi gwamnatin Burtaniya cewa wani kundin jagora ga jami'an leken asirin kasar dangane da yadda za su yi da fursunonin da ke tsare a kasashen waje ya sabawa dokokin kare hakkin bil-Adama.

Hukumar da ke kula da kare hakkin bil-Adama a kasar ta shaidawa Firayim Minista David Cameron cewa za ta kalubalanci gwamnatin a hukumance idan ba a sauya kundin ba, wanda aka wallafa a watan Yuli na bana.

An dai rubuta kundin ne a daidai lokacin da ake zargin cewa jami'an tsaron Burtaniya da na leken asiri na kasar na da hannu dumu-dumu a azabtar da wadanda ake zargi da aikata ta'addanci, wadanda ake tsare da su a kasashen Pakistan, da Afghanistan, da Morocco.

Kundin dai ya umurci jami'an da kada su yi tambayoyi ko su nemi bayanan sirri daga fursunonin da suka hakikance ko suka san cewa za a gana musu ukuba.

Sai dai hukumar kula da kare hakkin bil-Adaman ta ce kundin bai umurci jami'an da kada su ci gaba da yiwa wadanda ake zargin tambayoyi ba idan akwai yiwuwar azabtar da su.

A wata takarda da ta aikewa Firayim Minista Cameron, hukumar ta ce za ta kaddamar da bincike na shari’a in har ba ta samu gamsashshen bayani dangane da damuwarta nan da yammacin ranar Alhamis ba.

Ofishin Firayim Ministan Burtaniyar dai ya ce tanade-tanaden kundin sun dace da dokokin kasar da ma na kasa-da-kasa.

Wani kakakin ofishin ya ce ministoci ba za su ba da izinin aiwatar da duk wani abin da suka san cewa zai kai ga azabtar da mutane ba.