Zabtarewar kasa ta malale wani gari a Mexico

Yankin da zabtarewar kasa ta shafa a Mexico
Image caption Yankin da zabtarewar kasa ta shafa a Mexico

Hukumomi a Mexico sun ce gidajen da yawansu ya kai dari uku ne kasa ta binne, sakamakon zabtarewar laka, a dalilin ruwan sama kamar da bakin kwarya a wani gari dake jihar Oaxaca dake kudancin kasar.

Rahotannin da aka fara samu na nuna cewa abin ya zo wa mazauna garin Santa Maria Tlahuitoltepec,dake tsaunukan Oaxaca da ba-zata inda suka wayi gari da zabtarewar lakar da sanyin safiyar yau.

Yanzu haka sama da mutane dari ne baa ga ni ba a garin Santa Maria Tlahuitoltepec dake jahar Oaxaca.

Za dai a kwashe baki dayan mutanan garin amma kuma har yanzu masu aikin ceto na ta kokarin kaiwa wajen sa'o'i bayan afkuwar lamarin.