An sace yara 'yan makaranta 15 a Jihar Abia.

'Yan Sandan Nigeria
Image caption 'Yan Sandan Nigeria

Hukumomi da jami'an tsaro a Nigeria sun ce suna kokarin kubutar da wasu yara 'yan makaranta su 15 da ake zargin wasu 'yan bindiga sun sace a jihar Abia

Rahotanni sun ce an sace yaran ne a lokacin da suke cikin wata safa da ke kan hanyar zuwa makaranta.

Al'amarin ya afku ne a birnin kasuwanci na Aba da ke jihar Abia.

Ana ganin wata alama ce ta sabon salon da matsalar sace mutane ta dauka da kuma yadda al'amarin ke kara habaka a Jihar.

Hukumomi a Jihar ta Abia sun ce suna kokari haikan wajen shawo kan matsalar sace sacen mutane a jihar.

Tuni wadanda suka yi garkuwa da yaran suka nemi a biya su diyya ta Naira miliyan 20 gabanin su sallami yaran.