Magajin birnin Moscow ya ajiye aikinsa

Shugaban kasar Russia,Dmitri Medvedev
Image caption Shugaban kasar Russia ya umarci magajin birnin Moscow ya yi murabus

Shugaban kasar Russia, Dmitri Medvedev ya umurci magajin garin Moscow, Mista Yuri Luzhkov yayi murabus, a matsayin wani mataki da ake yiwa kallon ci gaba da danganta mai tsami dake tsakaninsu.

Fadar gwamnatin kasar ta ce, Mista Medvedev ya sanya hannu akan wata doka wacce ta tunbuke Yuri Luzhkov daga mukaminsa, saboda ya rasa aminci daga shugaban kasar.

Wannan sanarwar dai ta biyo bayan rade-radin da ake tayi na wasu makwanni dake cewa ana dab da tursasawa Mista Luzhkov yayi murabus, sakamakon rashin jituwa tsakaninsa da shugaba Medvedev.

Kafafen yada labaran kasar sun yi ta sukar Mista Luzhkov, abinda yasa ya fice daga kasar, saboda tararrabin makomarsa.Sai dai ya dawo, kana ya ce ba zai je ko'ina ba.

Amma a yanzu karshen magajin gari Luzhkov, mutumin da ya shafe shekaru goma sha takwas yana tashe a siyasar kasar yazo.

Shugaba Medvedev nada ikon sauke shi.Sai dai mutane kalilan na ganin cewa, ya yi hakan ne ba tare da samun goyon bayan Piraminista da,kuma babban dan siyasar kasar, Vladamir Putin ba