Tsuntsaye sun yi barna a Borno

Taswirar Najeriya
Image caption Tsuntsaye sun yi barna a Borno

Rahotanni daga Jihar Bornon Najeriya sun ce, manoma da dama ne suka yi asarar amfanin gonar da kimarsa ta kai miliyoyin Naira sakamakon farmakin da tsuntsaye jan baki suka kaiwa gonaki a kananan hukumomi bakwai da ke jihar.

Manoman sun koka kan yadda tsuntsayen ke yi musu barna.

Malam Dauda,wani manomi ne kuma ya ce:''Yau mun kai kimanin kwanaki goma muna korar wadannan tsuntsaye.Muna fama da wahalar noma,da kuma wahalar korar tsuntsaye''.

Manoman sun yi kira ga gwamnati ta agaza musu wajen tsayar da barnar da tsuntsayen ke yi musu.

Tsuntsayen, wadanda galibi sun fi rayuwa ne a wuri mai dausayi, kan taso ne daga gabar yankin Tafkin Chadi kowace shekara a daidai lokacin da manoman ke shirin girbe amfanin gona.