WHO ta wallafa rahoto akan cutar AIDS

AIDS
Image caption AIDS

Hukumar kula da lafiya ta duniya, WHO, ta ce an samu ci gaba akan yakin da ake yi da cutar nan mai karya garkuwar jiki watau AIDS, amma akwai sauran aiki.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wani rahoton hadin guiwa tare da asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya da kuma hukumar yaki da cutar AIDS ta majalisar.

Rahoton ya ce adadin mutanen da ke samun magunguna masu rage radadin cutar ya karu, inda a kasashe da dama, kusan dukkanin mutanen da ke bukatar magungunan suke samu.

Dama dai shekaru hudu da suka wuce ne kasashen dake cikin majalisar dinkin duniya suka gicciyawa kansu wa'adi na shekara ta 2010 domin tabbatar da ganin kashi tamanin na mutane masu dauke da kwayar cutar suna samun wadannan magunguna.

A da dai magungunan suna da matukar tsada, amma a yanzu farashinsu ya fadi warwas, abun da kuma ya taimaka matuka wajen samun ci gaba.

Rahoton ya ce tuni kasashe takwas, wadanda suka hada da Botsawana da Rwanda sun cimma wannan wa'adi.

To saidai rahoton yayi gargadin cewa matsalar tattalin arzikin da ake fuskanta, yana jefa mutanen dake dauke da kwayar cutar cikin mugun hadari.