An rufe makarantu da bankuna a Aba

'Yan sandan Nigeria
Image caption 'Yan sandan Nigeria

Rahotanni daga birnin Aba na jihar Abiya da ke kudu maso gabashin Najeriya sun ce, an rufe bankuna da makarantu da sauran harkokin kasuwanci a birnin, sakamakon kamarin matsalar yin garkuwa da jama'a, da fashi da makami, da dai sauran miyagun laifuffuka. Hakan na faruwa ne yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da kokarin kubutar da yaran nan 'yan makaranta su 15, wadanda aka sace a ranar Litinin, domin neman fansar kudi naira miliyan ashirin.

Mahukunta a Najeriya sun ce suna bakin kokarinsu, wajen shawo kan matsalar sace-sacen mutane da ke addabar al`umar kasar, duk kuwa da tayin afuwar da gwamnati ta yi wa masu irin wannan aika-aikar.