Bikin shan gishiri na kulla auratayya

Wasanni da rakuma a wajen bikin shan gishiri
Image caption Bikin shan gishiri na kulla auratayya

A Jamhuriyar Nijar, bikin sallar shan gishiri ta makiyaya da ake yi kowacce shekara a garin Ingall na jihar Agades dake Arewacin kasar, ya kasance wata dama inda samari ke samun sukunin kulla huldar auratayya tsakaninsu.

Mazaje har daga kasashen waje, ciki har da Najeriya kan halarci bukin da fatan samun matan aure.

Ranar Litinin da ta gabata ne dai aka kammala bukin da aka yi a bana, wanda manufarsa ita ce shayar da dabbobi gishiri da kuma ba su ciyawa masu warkaswa.

Makiyaya da 'yan kasuwa da masu yawon bude ido da dama ne suka halarci bikin