An yi zanga-zanga a kasashen turai

Zanga zanga a Brussels
Image caption Zanga zanga a Brussels

An yi zanga-zanga a yawancin kasashen nahiyar turai, inda masu zanga zangar ke bayyana fushinsu game da tsuke bakin aljihun da gwamnatocinsu ke yi.

Mafi girma cikin zanga zangar ita ce wadda da ake yi a birnin Brussels, inda dubban mutane suka yi jerin gwano a hedkwatar kungiyar tarayyar turai.

Ana yajin aiki a kasar Spain, a karo na farko a cikin shekaru 8. Zanga zangar da ake a Spain na shafar harkokin zirga zirgar jama'a da kwasar shara da kuma aikin kamfanin karafan kasar.

A kasashen Girka da Ireland da Italiya ma ana zanga zangar.