Wani bincike ya nuna jama'a na zaune kan Koguna masu barazana

Wani binciken koguna na duniya da aka gudanar, ya gano cewa kashi 80 cikin dari na mutanan duniya na zaune ne a kusa da kogunan dake fuskantar barazana.

Har ila yau binciken ya gono cewa kimanin mutane biliyan uku da rabi a kasashe masu tasowa na zaune a wuraren da ba tabbacin samun tsabtataccen ruwan sha. Masu bincinken sun dora alhakin rashin duba yadda za'a shawo kan matsalar rashin tsaftataccen ruwa kan kasashen da suka ci gaba, su ka kuma yi kira ga kasashe matalauta na su koyi darasi daga kura-kuran da kasashen Yamma suka yi.