Hukumar NAPTIP ta gano yan Nigeria masu karuwanci a Mali

Karuwanci
Image caption Karuwanci

Hukumar nan mai yaki da safarar mutane a Najeriyar, watau NAPTIP, ta ce ta gano dubban kananan 'yan mata, wadanda aka yi fataucinsu zuwa kasar Mali domin yin karuwanci.

Babban sakataren hukumar, Barista Simon Chuzi Egede, ya ce, masu fataucin na fakewa da dokokin Mali, wadanda suka hallata karuwanci ga 'yan matan da suka dara shekara 18, inda suke kara yawan shekarun kananan 'yan matan da basu kai sha takwas din ba.

Hukumar ta NAPTIP ta bukaci kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afirka ta kira taron gaggawa, domin sake nazari kan yarjajeniyar yaki da fataucin mutane.

Hukumar ta ce zata hada guiwa da ma'aikatan tsaro domin kama wadanda ke da alhakin yin wannan abu.