An sabunta: 29 ga Satumba, 2010 - An wallafa a 13:56 GMT

Cikar Najeriya shekaru 50: Shin za ku yi bukukuwa?

Tsohon Firimiyan Arewa Ahmadu Bello

Najeriya na da kabilu mabiya addinai daban-daban

Najeriya na bikin cika shekaru hamsin da samun 'yancin kai daga ranar 1 ga watan Oktoba. Shin za ku yi bukukuwa?

A lokacin da aka yi kasa da tutar Burtaniya, 'yan Najeriya da dama na cike da fatan cewa rayuwarsu za ta inganta da zarar sun karbi ragamar mulkin kansu.

Sai dai shekaru hamsin da samun 'yancin kan, mafiya yawan 'yan kasar na rayuwa cikin talauci, yayinda aka sace ko barnatar da dimbin arzikin man da Allah ya albarkace ta da shi.

Wasu na ganin a shekaru hamsin din da kasar ta shafe, babbar nasarar da ta samu ita ce ta kasancewa a matsayin kasa guda, duk da irin bambance-bambancen addini da kabilancin da ke tsakanin jama'ar kasar.

Shin kana zaune ne a Najeriya? Ko kuma dan Najeriya ne kai da ke zaune a wata kasar? Za mu so muji daga gareka. Ta yaya za ka yi bikin samun 'yancin kai? Me hakan ke nufi a gareka? Wanne irin sauyi aka samu a kasar cikin wadannan shekaru hamsin din?

Bayyana ra'ayinka ta hanyar cike wannan shafin:

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.