'Yan kwadago na yajin aiki a Spaniya

Zanga-zanga a Spain
Image caption Wani ma'aikaci na kona taya domin nuna fushi a birnin Barcelona na Spain

Kungiyoyin kwadago sun fara wani yajin aiki na gama-gari a kasar Spaniya domin nuna rashin amincewa da matakan tsuke bakin aljihun da gwamnatin kasar ke dauka. Hakan ya kuma yi daidai da zanga-zangar da ake yi a kasashen Turai da dama.

Yajin aikin na Spaniya ya kawo cikas ga harkokin sufuri da ayyuka a kasar, abinda ya jefa jama'a da dama cikin mawuyacin hali.

Masu zanga zanga daga kasashen duniya talatin ne za su yi jerin gwano a birnin Brussel, zuwa wasu cibiyoyin hukumomin kasashen Turai don nuna rashin jin dadinsu kan matakan tsuke bakin aljihu da kasashen Turai da dama ke dauka.

Mutane da dama sun rasa ayyukan yi tun bayan da aka fada matsalar tabarbarewar tattalin arziki, kuma ana gani gwamnatocin kasashen Turai da dama zasu ci gaba da tsuke bakin aljihunsu.

Masu zanga zangar sun kara da cewa, zasu tabbatar gwamnatocin sun aiwatar da sauye-sauye ga tatalin arzikinsu, ta yadda za a samu ayyukan yi.