Amurka ta sanyawa Iraniyawa 8 takunkumi

Takunkumin Amurka kan Iraniyawa 8
Image caption Amurka ta sanyawa Iraniyawa 8 takunkumi

Amurka ta sa sunayen wasu jami'an Iran 8 cikin jerin sunayen dake da kashin kaji, bisa zargen zargen da ake musu kan keta hakkin dan adam bayan zabenda aka gudanar a kasar mai cike da takaddama.

Sakatariyar kula da harkokin wajen Amurkan Hillary Clinton tace akan idanun wadannan jami'an ne aka rika kama Iraniyawa ana kullesu ana gallaza musu azaba, inda aka yi musu fyade, aka kuma kashe wasunsu.

Daga cikin jami'an takwas har da kwamandan dakarun juyin juya hali, Mohammad Ali Jafari, ministan cikin gida, Mostafa Mohammad Najjar da kuma mukaddashin shugaban yan sanda, Ahmad Reza Radan.

Takunkumin haramcin na kunshe ne da sa hannun shugaba Obama, wanda zai killace dukkanin dukiyar da suka mallaka a Amurka.