Alkalai a India sun raba wurin masallacin Ayodhya

Jami'an tsaro a Ayodhya
Image caption Jami'an tsaro a Ayodhya

Wata babbar kotu a arewacin Indiya ta yanke hukuncin cewa sashen wani masallaci da aka ruguje a Ayodha, wanda aka sha zubar da jini akan mallakar sa cewa a raba shi tsakanin 'yan Hindu da Musulmi.

Alkalan a birnin Lucknow sun ce wannan gurin ibada, wanda mabiya addinin Hindu suka lalata shekaru goma sha takwas da suka wuce, cewa a raba shi gida uku.

Hukuncin ya ce kashi biyu cikin uku na wannan guri za a baiwa 'yan Hindu ciki har da cibiyar gurin.

An tsananta tsaro kafin yanke hukuncin ganin cewa har yanzu jama'a basu manta mutanen da aka kashe ba sakamakon rikicin da aka yi a 1992.

Kimanin mutane dubu biyu ne mafi yawansu musulmai dai suka rasu a wata zanga zanga da ta barke bayan da aka rusa wani masallaci dake Ayodhya a shekarar 1992.