An yanke hukunci a kan Ayodhya a India

Masallacin Babri da Hindu suka rusa
Image caption Musulmi sun ce za su daukaka kara

Firaministan Indiya, Manmohan Singh, ya nemi jama'a da su kwantar da hakalinsu bayan wata kotu ta yanke hukunci kan wani gurin ibada da ake rikici a kansa, inda ta ce a raba shi tsakanin 'yan Hindu da Musulmi.

A bisa wannan hukunci, 'yan Hindun za su sami kashi biyu cikin uku a arewacin garin Ayodhya, inda wasu matasa suka yi barna a 1992 abinda ya jawo tarzomar da tai sanadiyyar rayuka dubu biyu.

Wata lauya, Nitya Ramakrishan ta shaidawa BBC cewa, wannan hukunci nasara ce ga bangaren 'yan Hindu.

Kotun ta yi kokari a sami matsaya da kowa zai amince da ita, amma hakan bai yiwu ba, da aka kasa filin gida uku.

Lauyoyin musulmi sun ce zasu daukaka kara, yayin da 'yan Hindu suka yabi hukuncin.