Makomar karatun yara a Najeriya

Wasu yara mata a Kaduna
Image caption Wasu yara mata da ke koyon karatu a jihar Kaduna

Najeriya ce kasar da tafi albarkatun mai da kuma yawan jama'a a nahiyar Afrika. Sai dai tana daya daga cikin kasashen da ke da tsarin ilimi mafi muni a duniya.

A garin Kaduna da ke Arewacin Najeriya, yara ne da shekarunsu basu fi goma ba, suke kaiwa-da-komowa a tsakanin motoci domin gogewa motocin dattin da ke gilashin su.

Sukan yi rige-rige domin neman aikin yaran mota, wanda ake kira Conductor a Turance.

Wani yaro dan shekaru 13 Aminu Haruna na daga cikin irin wadannan yara da ke yawo a titi.

Yaron ya shaidawa BBC cewa "Bani da ko kwabo, iyayena talakawa ne, shi yasa ka ganni a nan."

"Inaso na samu wani abu ne domin na taimakawa iyaye na."

Masu mototocin sun fi so su dauki yara kanana domin sune ba su da wayo sosai, kuma sun fi amana da kuzari.

"Ba mu da kima a idon mutane. Shi yasa nake so na koma makaranta domin na koyi abinda zan dogara da shi a nan gaba," a cewar Aminu.

Fiye da rabin yara miliyan 8 da doriya da ba sa zuwa makaranta na rayuwa ne a Arewacin kasar.

Image caption Yawancin matan da ke koyon sana'a anan zaurawa ne

Duk da yadda mahukunta a Najeriya suke ikirarin nasara a shirin samar da ilimin Firamare kyauta, kasa da kashi 50 cikin dari ne na yaran kasar ke halartar makaranta a Arewacin kasar. Kamar yadda binciken Campaign for Global Education ya nuna.

Hakan dai ba zai rasa alaka da yadda ake kin jinin ilimin boko a yankin ba.

Rukayyat Adamu

BBC ta ziyarci wata cibiyar koyawa mata sana'a, inda fiye da talatin daga cikin daliban yara ne mata wadanda aurensu ya mutu. "Talauci ne kawai ya jefa mu wannan hali," a cewar Rukayya, wacce ta kafa makarantar.

Idan aka koma kauye iyayensu ba sa iya daukar nauyin komai.

Da yawa daga cikin matan da suka zanta da BBC sun nuna takaici abisa auren da suka yi da wuri, wanda a cewarsu shi ne musabbabin halin da suka samu kansu a ciki yanzu.

'hadin baki da jami'ai'

Kimanin miliyan 75 na jama'ar kasar - fiye da rabin jama'ar yara ne - 'yan kasa da shekaru 18, kuma masana sunce ana sa ran za a haifi wasu karin miliyan 68 nan da shekara ta 2050.

A yanzu haka kashi daya daga cikin uku na wadanda suka kammala jami'a basu da aikin yi, kuma masana naganin wajibi ne tattalin arzikin kasar ya bunkasa domin samarwa da wadannan matasan aikin yi.

Wani abin da kekara tabarbara harkar ilimi shi ne yadda ake karkatar da kayan aiki domin siyarwa a kasuwannin bayan fage, abinda malaman ke cewa yana yin cikas ga ayyukansu.

"Abin yana bakantamin rai," a cewar Zakari. " Wannan litattafan kamata yayi ace an rabasu kyauta a makarantu.

Wasu daga cikin litattafan wadanda na Turanci ne an rubuta cewa "ba na sayarwa bane" kuma "mallakar gwamnatin tarayyar Najeriya ne".

Malam Zakari ya kara da cewa jami'an gwamnati na hada baki da baragurbin 'yan kasuwa domin cutar da al'umma.

" Abin da gwamnati ke samarawa ba ya isa, ba ya zuwa inda ya kamata," a cewar Zakari cikin fushi.

" Ana matukar cutar da miliyoyin yara a Najeriya."

Karin bayani