NATO ta tabbatar jirginta ya shiga sararin samaniyar Pakistan

Dakarun kungiyar kawance ta NATO sun tabbatar da cewa daya daga cikin jiragensu mai saukar ungulu ya shiga sararin samaniyar kasar Pakistan ranar alhamis.

NATO ta ce wannan jirgin ya shiga sararin samaniyar ne domin neman masu tayar da kayar baya, da kuma bude wuta domin kare kai.

Ministan cikin gida na Pakistan ya nuna rashin jin dadinsa.