A Nijar kwamitin rijistar masu zabe ya mika kundin masu kada kuri'a

Hukumar zabe mai zaman kanta a Niger, CENI, ta mikawa gwamnatin kasar rajistar wadanda suka cancanci jefa kuri'a a babban zabe mai zuwa.

Fiye da mutane miliyan shida da dubu dari bakwai ne rajistar ta kunsa.

Bisa alkawarin da kwamitin ya dauka tun farko a yau ne wa'adin mika girgam din na zabe.

Shugaban Kwamitin, Malam Musa Abdu ya bayyana farin cikinsa na kammala aikin cikin lokaci da kuma nasara.

Sai dai wasu jama'iyun sun bayyana cewar sun gamsu da sakamakon rijistar amma kuma idan da an yi aikin a cikin lokaci mai yawa da an samu karin mutanen da suka cancanci kada kuri'a.

Kwamiti mai rajistar masu zaben ya kwashe watanni ukku yana aikin, kuma a yau ne aka tsara zai mika sakamakon aikin nasa ga gwamnati.