Ana ci gaba da bukukuwan cikar Najeriya shekaru hamsin

A ci gaba da shagulgulan cikar Najeriya shekaru hamsin da samun mulkin kai daga Birtaniya, a yau an shirya wata lacca a Abuja, domin duba irin rawar da kasar take takawa a fagen shugabanci a nahiyar Afirka.

Gwamnatin Najeriyar da ma wasu kasashen takwarorinta, sun yaba da irin gudunmawar da kasar ta bayar, a fafitikar 'yantarwa, da kuma wanzar da zaman lafiya a sassa daban-daban na nahiyar Afirka.

Minista a ma'aikatar harkokin waje ta Najeriya, Dr Aliyu Idi Hong, ya bayyana irin kokarin da Najeriyar ta yi wajen tallawa wasu kasashe na Afrika samun yancin kai da kuma zaman lafiya.

Haka nan kuma Shugabar Liberia, Allen Johnson Sirleaf da kuma tsohon Shugaban Afrika ta Kudu, Thabo Mbeki sun yaba da irin rawar da kasar ta taka a fagen kyautata lamura a kasashen Afrika da duniya baki daya.