An wallafa hotunan mai jiran gadon Shugabancin Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa ta saki hotunan Kim Jong-un, dan autan shugaba Kim Jong-il, wanda kuma ake ganin shi ne zai gaje shi.

Hotunan sun nuna wani matashi da fuska daure yana zaune da jiga-jigan jam'iyyar dake mulki a Koriya ta Arewa.

Daga cikin abubuwan da suke jan hankali dai akwai shirin nukilya na Koriya ta Arewa.

A cewar ak Kil-yon, mataimakin ministan harkokin waje na Koriya ta arewa, halin da ake ciki a arewa maso gabashin Asiya ya nuna cewa Amruka ba a bar dogaro ba ce.

Daga baya kuma an nuna Kim Jong-un a akwatinan Talabijin yana ta tafi a taron jam'iyyar, inda kuma aka maida shi janar din soja mai anini hudu da kuma manyan mukaman jam'iyya guda biyu.

Wata tawaga ta Koriya ta Arewa ta nufi kasar China, inda ake sa ran zasu yi jami'ai a kasar ta Sin bayani kan wannan mataki.