Za a saurari ba'asi kan kasar Congo

Wata mace da akei zargin yiwa fyade a Congo
Image caption Za a saurari ba'asi kan lalata a Congo

Wani kwamiti da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa zai fara sauraron ba'asi wajen matan da aka yi lalata dasu a jamhuriyar Dimokaradiyar Congo.

Matan da aka yi lalatar dasu zasu bada ba'asi kan irin abubuwan da suka yi ta fama dasu, musamman ta fannin shari'a da kuma yadda abin ya shafi tunaninsu.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya ce, hakan wata dama ce da zata sa wadanda a ka yi lalatar da su fitar da kuncin dake zukatansu.

Kwamitin zai ziyarci wasu yankuna a gabashi da kuma kudancin kasar, inda zai ji ba'asin jama'a fiye da dari cikin kwanaki goma. Dubban mata ne dai ake yi wa fyade a kasar Congo a duk shekara, sai dai ba safai ake yi musu adalci ba.