An sako 'yan makarantar da aka kama a Abia

Jami'an 'yansandan Najeriya
Image caption Harkokin tsaro na daga cikin abubuwan da ake nuna shakku a kansu

Jami'an 'yanasanda a Najeriya sun sami nasarar ceto yaran nan 'yan makaranta 15, wadanda wasu 'yan bindiga suka sace a cikin mota a kan hanyarsu ta zuwa makaranta a ranar Litinin din da ta gabata.

Mista Ogbonna Geofrey, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Abiya, wanda ya tabbatar wa da BBC, ya ce 'yan bindigar sun gudu ne sun bar yaran a maboyarsu, sakamakon matsin lambar samamen da wata rundunar hadin gwiwa ta sojoji da 'yan sanda ta kai wajen.

Jami'in ya kara da cewa an sami yaran ne cikin koshin lafiya a wani daji da ke yankin Ngwa na jihar Abiya. Kuma ba a biya wasu kudin fansa ba. Kame jama'a a yi garkuwa da su domin neman fansa ya zamo ruwan dare a yankin Kudu maso Gabashin kasar da ma wasu sassa, duk da irin matakan da hukumomi ke cewa suna dauka domin kawo karshen matsalar.