Harin bom ya kashe mutane 8 a Najeriya

Bom ya kashe mutane da dama a Najeriya
Image caption Harin yazo ne lokacin da ake bikin cikar Najeriya shekaru 50 da samun 'yancin kai

Akalla mutane takwas ne suka mutu bayanda wasu bama-bamai suka tashi a kusa da wajen da ake bikin murnar cikar Najeriya shekaru 50 da samun 'yancin kai.

Majiyar 'yansanda ta tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Reuters faruwar abin. Inda ta kara da cewa mutane takwas sun mutu kawo yanzu, ciki har da jami'an 'yansanda.

Amma wani ma'aikacin hukumar kashe gobara ya shaidawa BBC cewa sun gano gawarwaki goma.

Bama-bamai biyu ne suka tashi wadanda suka lalata motoci uku, tare da jiwa wasu mutanen raunuka.

Sai dai an ci gaba da shagulgulan murnar ranar samun 'yancin kan kamar yadda aka tsara.

Harin ya zo ne mintuna kadan bayanda kungiyar MEND mai fafutukar kwato yankin Niger-Delta, ta yi gargadin cewa za ta kai hare-hare a wajen bikin samun 'yancin kan.

Kungiyar Mend tace jami'anta da ke aiki a cikin rundunar 'yan sandan kasar ne suka dasa bama-bamai a wasu motoci da ke wurare daban daban.

Gani da ido

Editan BBC a Abuja Ahmed Idris ya ce ya ga kafafuwan mutane sun yi jina-jina a wurin da abin ya faru, yayinda ma'aikatan agaji ke kokarin sasu a motoci.

Wakilinmu ya kara da cewa akwai yiwuwar wani bom din na uku ya kara tashi a filin da ake taron. Da farko jami'an tsaro a wajen sun ce bindiga ce ta tashi.

Image caption Yansanda na binciken wurin da harin ya faru

Bama-baman biyu sun tashi ne da tsiran minti biyar kawai a tsakaninsu. Yansanda suka ce bom na biyu ne ya yiwa mutane illa bayanda suka zo kallon na faro.

A shekarar da ta gabata, gwamnatin Najeriya ta yiwa masu fafutukar afuwa, inda aka yi musu alkawarin kudi da aikin yi domin su a jiye makamansu.

Kuma tun daga lokacin ne sace-sacen jama'a da hare-hare kan kamfanonin hakar mai ya ragu, sai dai wasu daga cikinsu sun yi korafin cewa gwamnati ta ki cika musu alkawarin da ta yi.

Kuma aikin hakar mai ya karu tun bayanda aka fara aiki da shirin afuwar - daga miliyan daya da rabi zuwa kusan miliyan biyu.

Shugaba Jonathan wanda ya fito daga yankin na Niger-Delta. Ya yi alkawarin kawo karshen matsalar bayanda ya hau karagar mulki, kuma wani jami'in masu fafutukar ya shaidawa BBC cewa shugaban ne ya fi kowa cancanta da ya shawo kan matsalar saboda dan yankin ne.