Majalisar dinkin duniya ta ce kisan yan Hutu a Congo kisan kare dangi ne

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan kashe-kashen da aka yi a Jamhuriyar Dimukuradiyya ta Kongo a rikicin da aka shafe sama da shekaru goma ana yi, ya nuna cewa sojojin Rwanda na da hannu a kisan da aka yiwa fararen hula 'yan Hutu, wanda idan aka tabbatar a kotu zai iya zama kisan kare dangi.

Rahoton ya ce kashe dubunnan mutanen da aka yi lokacin gumurzun, an yi shi ne da gayya, domin kuwa an tsara shi, sannan aka yanke hanzari, bugu da kari kuma ya yadu.

Rahoton ya zargi wasu karin kasashe biyar da hannu wajen kisan 'yan Hutun a tsakanin shekara ta 1993 zuwa shekara ta 2003.

Rahoton ya bayar da shawara ga gwamantin Kongo da ta nemi hanyoyin gabatar da wadanda ake zargi a gaban Kuliya.