Shugaban Ecuador ya yi jawabi ga 'yan kasar

Shugaban Ecuador Rafael Correa
Image caption Shugaban Rafael Correa yana jawabi ga jama'ar kasar

Shugaban Ecuador Rafael Correa ya gabatar da jawabi ta akwatunan talabijin inda ya yi alkawarin ladaftar da wadanda suka shirya abinda ya kira yunkurin juyin mulki.

Ya ce ba za a manta ko kuma yafe wa wadanda suka shirya wannan bore ba wanda ya sa aka kai masa hari da barkonon tsohuwa, kuma ya ritsa da shi a wani asibiti har sai da sojoji suka kwato shi.

Wakilin BBC ya ce, da yin wannan tarzoma sai shugaban Ecuador din, kuma amininsa Hugo Chavez na Venezuela suka ce wani yunkuri ne na juyin mulki.

Tun da farko dai shugaban kasar ya sanya dokar ta baci bayan da wasu bijirarrun 'yan sanda da sojoji suka karbe iko a filin jirgin saman babban birnin kasar, inda kuma suka bazu a wasu sassan birnin don nuna adawarsu da matakin rage musu kudaden salala da shugaban kasar ke shirin yi.