An sallami shugaban Ecuador daga asibiti

Shugaban Ecuador,Rafael Correa(a tsakiya)
Image caption An sallamo shugaba Correa daga asibiti

An sallami shugaba Rafael Correa na Ecuador daga asibiti, bayan da wasu 'yan sanda suka harba masa hayaki mai sa hawaye, sakamakon wata takaddama da ta kaure a tsakaninsu.

Sojoji sun yi amfani da karfin tuwo wajen kubuto shugaban kasar inda aka yi ta jin harbe harben bindiga a babban birnin kasar.

An dai yi ta murna a harabar fadar shugaban kasar inda Mista Correa yayi jawabi ga dimbin jama'a, inda da ya shaida musu cewa an kashe mutum guda a hatsaniyar.

Tun da farko dai shugaban kasar ya sanya dokar ta-baci bayan da wasu bijirarrun 'yan sanda da sojoji suka karbe iko a filin jirgin saman babban birnin kasar, kuma suka bazu a wasu sassan birnin don nuna adawarsu da matakin rage musu kudaden salala da shugaban kasar ke shirin yi.