Uganda ta mika wuya

Taswirar kasar Uganda
Image caption Uganda ta mika wuya ga bukatar majilisar Dinkin Duniya

Uganda ta ce zata ci gaba da kasancewa cikin rundunar wanzar da zaman lafiya ta kasashen Afrika duk kuwa da nuna rashin jin dadinta game da wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da za'a fitar a ranar juma'a.

Rahoton dai ya zargi sojojin kasar ta Uganda ne da cin zarafin fararen hula a lokacin rikice rikicen Jamhuriyar Demukradiyar Congo.

Har ila yau, rahoton ya kuma yi irin wannan zargi ga kasar Rwanda lamarin daya fusata kasashen biyu.

Hakan yasa kasar ta yi barazanar ficewa daga rundunar wanzar da zaman lafiyar.