Amurka tayi tir da bama baman da suka tashi a Najeriya

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Gwamnatin Amurka tayi Allah-wadai ta bama baman da suka tashi a Abuja, yayin gudanar da bukukuwan cika shekaru hamsin da samun 'yancin kan kasar

Gwamnatin Amurka tace, tashin bama-baman da aka dana a ranar Jumma'a a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, na nuna muhimmancin yin sahihin zabe badi a Najeriya.

Kakakin ma'aikatar hulda da kasashen wajen Amurkan, P. J. Crowley ya kuma ce, gwamnatin Amurkan na yin Allah-wadai da tada bama-baman da suka yi barna, a daidai lokacin da Najeriyar ke yin bukukuwan cika shekaru hamsin da samun 'yan cin kai.

Lamarin dai ya kai ga hallaka mutane takwas, kuma tuni kungiyar nan mai ikirarin fafutukar 'yan to yankin Niger-Delta mai arzikin mai, wato MEND tace, ita ke da alhakin dana bam din.