An yi bikin bude wasannin Kwamanwelz a Indiya

A Delhi, babban birnin kasar Indiya, Yerima Charles, mai jiran gadon sarautar Birtaniya, da kuma shugaban kasar Indiyar, Pratibha Patil sun bude gasa ta goma sha tara ta kungiyar kasashen kwamanwelz.

Daruruwan makada da maraya ne suka cashe, a bikin bude gasar, wanda aka gudanar a filin wasa na Jawaharlal Nehru, wanda ya cika ya batse da 'yan kallo, inda aka nuna al'adu daban daban na kasar ta Indiya.

Dubban 'yan wasa ne daga kasashe saba'in da daya, zasu fafata a gasar wasannin, wadanda za a gudanar karkashin tsauraran matakan tsaro.