Masar da Iran za su dawo da zirga-zirgar jirage

Taswirar kasar Masar
Image caption Taswirar kasar Masar

A karon farko cikin shekaru talatin, kasashen Masar da Iran sun amince su mayar da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakanin manyan biranen juna, bayan wata tattaunawa a Masar.

Wakilayar BBC ta ce, yarjejeniyar zata bada damar jiragen fasinja su rika sawu ashirin da takwas a kowane mako, tsakanin Alkahira da Tehran.

Ba a bada karin haske kan lokacin da za a fara zirga-zirgar ba.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta tabarbare ne a 1980 , a lokacin ganiyar juyin-juyahalin Islama a kasar Iran, da kuma yadda Masar ta amince da Isra'ila a matsayin kasa.

Dangantaka ta ci gaba da kasancewa mai rauni tun daga lokacin, amma kafafen yada labaran Iran sun ce ana ganin matakin a matsayin wani share fage na dawo da dangantaka tsakaninsu.