Kudancin Sudan zai zabi ballewa daga Sudan

Sojojin kudancin kasar Sudan
Image caption Kudancin kasar Sudan na bukatar ballewa daga hadaddiyar kasar Sudan a zaben raba gardamar da za'ayi a watan Janairu

Shugaban yankin kudancin Sudan, Salva Kiir ya nuna cewar shi fa ba zai zabi cigaba da kasancewar yankin a matsayin wani bangare na hadaddiyar kasar Sudan ba, a zaben raba-gardamar da za'ayi a watan Janairun badi.

Kuma ya kara da cewar, bai ga wani dalili ba da zai sa yayi sha'awar ganin yankin na kudancin Sudan ya cigaba da kasancewa wani bangare na hadaddiyar kasar ta Sudan ba.

Amma daga bisani wani mataimaki na musamman ga Salva Kiir ya dage cewar, wadannan kalamai ba wai suna nuna kuri'ar da shugaban zai kada ba ne.