Mun garagadi gwamanatin Nijeriya kafin kai hari-inji MEND

Kungiyar mayakan sa kan nan ta Nijeriya wadda ta ce ita ce ta tayar da bama bamai ranar Juma'a, a lokacin bukukuwan cikar kasar shekaru hamsin da samun 'yancin kai, ta ce ta sanar da hukumomi game da hare-haren, kwanaki biyar kafin ta kai su.

Bama-baman dai sun halaka mutane akalla goma sha biyu.

Wakilin BBC ya ce a wata sanarwa da kungiyar ta MEND ta fitar, ta ce da an dauki matakan da suka dace, da ba a samu asarar rayuka ba.

Ta ce matakin da hukumomin Nijeriyar suka dauka, bayan gargadin shi ne na cin zarafin jagoransu dake gudun hijira a Afrika ta Kudu, Henry Okah.

Wasu manyan mutane da aka gayyata daga Birtaniya domin halartar bukukuwan dai sun soke halarta.