Amurka zata gargadi 'yan kasarta masu yawan bude ido

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Kasar Amurka zata na shirin daukar mataki domin kaucewa hare haren 'yan Al-Qaida

Gwamnatin Amurka zata fitar da wani sabon gargadi ga 'yan kasar dake zuwa yawon shakatawa kasashen Turai.

Sabon gargadin dai zai kuma bukaci Amurkawan su rika yin taka tsan-tsan saboda barazanar hare-haren 'yan kungiyar Al-Qaeda

Wani babban jami'in gwamnatin Birtaniya ya tabbatar da cewar, gwamnatin Amurka na shirin jan kunnen 'yan kasar dan su guji shiga taron jama'a a Birtaniya da ma sauran kasashen Turai.

Hukumomin tsaro dai na cewa, akwai wani shirin Al-Qaeda na kai hare-hare a wasu biranen kasashen Turai.