Bama baman da suka tashi a Abuja sun haifar da mahawara

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Ana samun bayanai masu karo da juna dangane da hare haren boma boman da aka kai a ranar da kasar ke bikin samun 'yancin kai

A Najeriya wata muhawara ta kaure dangane da hare-haren bom din da suka hallaka jama'a da dama a babban birnin kasar, lokacin da ake bikin cika shekaru hamsin da samun mulkin kai.

Muhawarar dai ta kaure ne sakamakon furucin da gwamnatin Najeriyar ta yi cewa 'yan ta'adda ne suka kai harin, sabanin ikirarin da kungiyar masu fafitikar 'yanta yankin Niger-delta, wato MEND tayi cewar, ita ce ta kai hare-haren.

Wasu dai na ganin cewa furucin shugaban kasar kan wannan batu bai dace ba.

A ranar juma'ar da ta gabata ne dai bama-bamai biyu suka tashi a kusa da dandalin Eagle Square, jim kadan bayan shugaban kasar ya duba sahun jami'an tsaron da suka yi pareti.