Afirka na samun bunkasar tattalin arziki

Kididdigar shekara shekara kan yanayin gwamnatoci a nahiyar Afirka, ta nuna cewa an samu ci gaban tattalin arziki, amma a 'yan shekarun baya bayan nan an samu koma baya ta bangaren demokradiyya.

Kididdigar wadda wani attajiri a kasar Sudan, Mo Ibrahim ya dauki nauyi, ta nuna cewa yawancin kasashen Afirka sun ba kasashen Turai rata ta bangaren habakar tattalin arziki.

A yanzu haka dai an shiga shekara ta hudu kenan a wannan kiddidgar, wadda ke auna dukkanin wasu alkaluma na yadda nahiyar Africa ke ci gaba, wadanda suka kama daga yawan yaran da ake dauka a makarantun Piramare, zuwa yawan farar hular da ake hallakawa a wuraren yaki.

A takaice abunda wannan bincike ya nuna shine a fannin tattalin arziki, an samu ci gaba mai armashi.