Za'ayi zagaye na biyu na zaben shugabakasar Brazil

'Yan takarar kujerar shugabancin kasar Brazil biyu
Image caption Za'a shiga zagaye na biyu na zaben shugabankasar Brazil a karshen watan daake ciki

Bayan da aka kammala kirga fiye da kashi casa'in cikin dari na gabakidayan kuri'un da aka kada a babban zaben kasar Brazil, yanzu haka ta tabbata cewar za'a yi zagaye na biyu na zaben shugaban kasar a ranar lahadin karshen wannan watan.

Duk da cewa 'yar takarar jam'iyyar Workers Party mai mulkin kasar, Dilma Rousseff ce ta lashe mafi yawan kuri'un da aka kada jiya, sai dai ta gaza samun gagarumin rinjayen da zai bata nasara kai tsaye

Kafin dai 'yan kwanakin da suka gabata, ba a tunanin cewar sai an je zagaye na biyu a wannan zabe, amma a lokacin yakin neman zabe ne 'yar takarar jam'iyya mai mulki ta rasa goyon bayan wasu masu ayukan yada addinin Krirista da basu gamsu ba da ra'ayinta dangane da batun zubar da ciki.

Dilma Roussef dai mai shekaru sittin da biyu a duniya ta taba zaman gidan yari a lokacin gwamantin mulkin soji