Geert Wilders zai fuskanci shari'a a Holland

Geert Wilders
Image caption Sanannen dan majalisar dokokin kasar Holland Geert Wilders mai nuna kiyayya ga addinin Islama zai fuskanci shari'ah

Sanannen dan majalisar dokokin kasar Holland din nan da yayi fice wajen nuna kiyayya ga addinin musulunci zai gurfana yau a gaban wata kotu bisa tuhumar tunzura mutane su kyamaci musulmi.

Shi dai Geert Wilders ka iya fuskantar daurin har tsawon shekara guda a gidan kaso, idan aka same shi da laifin da ya shafi wani wani fim da ya shirya mai suna Fitna, wanda a cikinsa yayi batanci ga Al-Quar'ani mai tsarki

Saboda yawan barazanar kisan da Geert Wilders ke fuskanta, a ko yaushe yana kewaye ne da jami'an dake tsaron lafiyarsa.