'Yan bindiga a Pakistan sun kaiwa motocin NATO hari

Motocin daukar mai na NATO na ci da wuta
Image caption 'Yan bindiga sun kaiwa motocin daukar mai na NATO hari a Pakistan

Wasu da ake zaton masu tada kayar baya ne a Pakistan sun kai hari, kana su yi kaca-kaca da tankunan mai fiye da ashirin da biyar dake samar da mai ga dakarun kungiyar tsaro ta NATO a Afghanistan.

Ma'aikatan asibiti dai sun ce, a kalla mutane shida ne suka mutu sakamakon harin da aka kai a kusa da babban birnin kasar na Islamabad.

Wannan hari dai shi ne na biyu tun daga ranar Jumma'a, yayin da hukumomin Pakistan din suka rufe wata babbar hanyar safarar muhimman bukatun dakarun rundunar tsaron ta NATO dake Afghanistan.