Ana daf da fito da mahakan ma'dinan kasar Chile su 33

Kayayyakin aikin fito da mahakan ma'dinan kasar Chile
Image caption Injiniyoyi sunce nan da karshen makon da ake ciki za'a fito da mahakan ma'adinan su 33 da suka makale a karkashin kasa

Injiniyoyi dake haka wata hanya da zata kai ga ma'aikatan hakar ma'adinan da suka makale a karkashin a kasa a Chile, sun ce, za'a iya ceto mutanen nan da karshen wannan makon.

Daya daga cikin shugabannin masu aikin hakar hanyar kaiwa ga wadanda suka makale a karkashin kasar yace, yanzu tsakaninsu da wurin da mutanen suke bai wuce mita dari da sittin ba:

zaman jiran tsammani na kwanaki sittin da dangin mutanen suke yi, ya kusan zuwa karshe kenan.

Tun farko dai shugaban kasar ta Chile, Sebastian Pinera yace, masu aikin ceto na daf da kubuto da mutanen